Latest:
Labarai

An Jibgi Kwamishina A Wajen Rabon Kayan Tallafi A Ondo

 

Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Ondo, Olubunmi Osadahun, ta sha dukan tsiya yayin rabon kayan tallafim rage radadin cire tallafin mai a yankin Arigidi Akoko na Jihar.

Lamarin ya faru ne a karshen mako, inda ake zargin mambobin jam’iyyar APC a yankin da yin dukan, bayan sun yi zargin ana kumbiya-kumbiya a rabon.

A wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 15 da Aminiya ta gani, an ga wani fusataccen mutum mai suna Awolumate Olumide, wanda aka fi sani da ‘Cuba’, wanda kuma shi ne shugaban APC na gundumar Akoko ta Arewa maso Yamma 1 yana duka Kwamishinar.

Mutumin dai ya yi amfani da kujera wajen kai mata duka a ka, lamarin da ya sa kan nata ya kumbura.

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa rashin fahimtar ta fara ne lokacin da wasu kusoshin APC suka yi zargin ba a gudanar da harkar rabon a fili.

Hakan ce ta sa Olumide ya nuna rashin gamsuwarsa da rabon, inda ya zargi Kwamishinar da mayar da shi saniyar ware.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kwamishinar, amma hakan ya ci tura saboda lambarta ba ta shiga har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Kazalika, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce har yanzu ba su kai ga samun rahoton lamarin ba tukunna.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply