Latest:
Labarai

An kashe mutum 3 a wani harin ƴan bindiga a Sokoto

 

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe mutum uku wasu sun samu raunuka a wani sabon harin da suka kai a yankin Soro da ke a karamar hukumar Binji, a jihar Sakkwato. 

Kakakin runudanar ‘yansandan jihar, Ahmad Rufai ne, ya tabbatar da kai harin wanda ya ce, ya auku ne a ranar Litinin.

A cewar Ahmad, ‘yan bindigar sun kaddamar da harin ne a yankin Soro, amma jami’an rundunar tare da taimakon jami’an soji, sun samu nasarar dakile harin ‘yan bindigar.

Kazalika ya ce, ‘yan bindigar sun kuma banka wa wasu gidaje wuta, wanda sakamakon hakan mutum uku suka rasu, wasu kuma suka samu raunuka.

Wasu majiyoyi a yankin sun bayyana cewa, maharan sun sace mutane da dama tare da kuma banka wa wasu gidaje wuta.

Bugu da kari, wasu mazauna yankin sun bayyana cewa, wasu ‘yan sintiri a yankin ne suka dakile harin ‘yan bindigar, wanda daga baya kwamishinan ‘yansandan jihar ya shiga tsakani domin tattaunawa da mazauna yankin.

Jaridar leadership