Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da sauke manyan Sarakunan Jihar guda biyu da Magajin Gari saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe ta.
Sanarwar da Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya gabatar tace an Sauke Sarkin Zurmi Atiku Abubakar da na Dansadau Hussaini Umar saboda yadda rahotan binciken da akayi ya tabbatar da laifi akan su.
Sanarwar dake dauke da sanya hannu Malam Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan tace an kuma sauke Suleiman Ibrahim Danyabi a matsayin Magajin Garin Birni Tsaba.
Sanarwar tace an dauki matakin sauke Sarakunan ne biyo bayan taron majalisar zartarwa wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar Hassan Nasiha ya jagoranta wanda ya amince da shawarwarin wani kwamitin bincike da ya gano hannun wadannan Sarakuna cikin matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Kafin dai wannan lokaci an dakatar da wadannan Sarakunan daga aiki saboda zargin da ake musu.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.