Home Labarai An kulle Masallacin Jumma’a kan rikicin limancin a Lagos

An kulle Masallacin Jumma’a kan rikicin limancin a Lagos

 

An samu rashin jituwa akan mukamin babban liman a Masallacin Epe da ke a jihar Legas, inda daya daga cikin rassan Masallacin da ke a jihar limamai biyu suke yi ikirarin su ne manyan limaman Masallacin.

Rashin jituwar wadda ta kunno kai a lokacin Sallar Juma’ar da ta gabata, lamarin ya faru ne a yayin da limaman biyu, suka yi yinkurin jagoranrar Sallar ta Juma’a wanda hakan ya janyo cacar baki da wuce gona da iri.

Babban Masallacin wanda ke a yankin Opo, rashin jituwar ya janyo mataimakin Sifeta Janar na ‘yansansa na shiyya ta biyu ya bayar da umarni a kulle Masallacin har sai an lalubo da mafita kan rikicin.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta na zamani, ya nuna yadda jami’an ‘yansanda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin, Alhaji Abdullateef Oladapo.

Hakan ya biyo bayan yadda limaman Masallacin biyu suka kasance a cikin Masallacin a lokacin Sallar ta Juma’a, ciki har da Alhaji Abdulkabir Oriyomi wanda ya nuna son jagorantar Sallar ta ranar Juma’a 22 ga watan Satumbar 2023.

Kazalika, an ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta karkashin ofishin mataimakin gwamnan jihar Dakta Obafemi Hamzat, ya tura jami’an ‘yansansa zuwa Masallacin don su tabbatar da bin doka da oda.

An ruwaito cewa, an nada Oladapo a matayin babban limamin Masallacin ne biyo bayan wata takardama a shekarar 2012 wadda ta yi sanadiyyar aka mayar da Oriyomi zuwa wani Masallacin da ke a gundumar Epe.

Jaridar Leadership


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.