Home Labarai An Lakada Duka Wa ‘Yan Jaridar Zimbabwe

An Lakada Duka Wa ‘Yan Jaridar Zimbabwe

Mahukunta a Zimbabwe sun buƙaci a gudanar da bincike a kan mummunan dukan da aka yi wa wasu ‘yan jarida hudu a kasar.

Kwamitin da ke kare ‘yancin ‘yan jarida a kasar ya ce an kai wa manema labaran hari ne bayan sun dauki bidiyon wani ayarin jerin gwanon motocin magoya bayan jam’iyyar Zanu-PF da ke mulkin kasar wadanda suka toshe wata babbar hanya a garin Gokwe da ke yammacin babban birnin kasar Harare in da suke wani gangami.

‘Yan jaridar na cikin daukar bidiyon ne sai kawai wasu mutum 10 daga cikin ayarin mutanen suka sakko daga motocinsu suka fara dukan ‘yan jaridar tare da ba su umarnin goge abin da suka dauka da kuma kwace musu makullan mota.

Daya daga cikin ‘yan jaridar ya shaida wa BBC cewa, an masa duka aka abin da ya sa ya rasa hakorinsa daya.

Dan jaridar ya ce daya abokin aikin na su ma sumar da shi aka yi tare da karya masa kafa.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.