Labarai

Ambaliya: Ƴan Kasuwar Kantin Kwari Sun Tafka Asara

Yan kasuwa a shahararriyar kasuwar nan ta Kantin Kwari a Jihar Kano sun koka kan asarar dukiyoyi da suka yi sakamakon ambaliyar ruwa.

Wakiliyar Radio Nigeria da ta zagaya kasuwar ta lura cewa ƴan kasuwa da dama suna kwashe kayayyakin da ke shagunansu.

Rahoton ya nuna cewa, ambaliyar ta afku ne bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren ranar Laraba, yayin da aka toshe mafi yawan magudanan ruwa a kasuwar.

Sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki domin sun yi asarar kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.

Kwamared Balarabe Tatari, shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwa kanana da matsakaita na kantin kwarin, ya yi magana kan yadda suka yi hasashen faruwar irin wannan bala’i a lokacin da aka gina sabbin gine-gine a layin Ta’anbo da kuma layin Bayajidda.

Ya ci gaba da cewa, duk kokarin da kungiyar ta yi don ganin an yi wani abu game da lamarin ya ci tura. Ya ce rashin tsarin sufuri da hanyoyin ruwa a cikin kasuwar ya taimaka wajen ambaliya da sauran hadurran muhalli.

Alhaji Balarabe ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da daukar matakin da ya dace domin dakile faruwar lamarin nan gaba.

A halin da ake ciki, shugabann hukumar da ke kula da Kantin kwari, Alhaji Abba Muhammad Bello ya musanta cewa gine-ginen sun toshe hanyoyin ruwa. Ya ce an rufe wasu magudanun ruwa ne na wani dan lokaci saboda aikin da ake yi a kasuwar.

Ya jaddada cewa hukumar za ta mika cikakken rahoto ga gwamnati domin daukar matakin da ya dace.

Idan za a iya tunawa, a watan Agustan 2021, ‘yan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin gamsuwarsu da wani gini da ake ginawa a Layin Ta Anbo a cikin kasuwar.

Sun yi nuni da cewa Layin Ta Anbo na daya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar kayayyaki a cikin kasuwar sannan tasha ce da ke hada magudanun ruwa.

Leave a Reply