Home Labarai Ba Mu San Yaushe Akayi Zama Da Ministan Kwadago Ba – ASUU

Ba Mu San Yaushe Akayi Zama Da Ministan Kwadago Ba – ASUU

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta ASUU a Najeriya ya ce ba su samu wata sanarwa daga gwamnatin kasar ba kan zama da Ministan Kwadago, da nufin kawo karshen yajin aikin da suke yi.

Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fada wa BBC cewa Ministan Kwadago, Chirs Ngige, ne ma ya yi watsi da tattaunawar, ya kuma dakatar musu da albashi da tunanin cewa hakan zai sa su sauya matsayarsu.

A jiya Laraba ne Mista Ngige ya shaida wa manema labarai cewa za su yi wani zama da wakilan ASUU yau Alhamis da nufin kawo karshen tirka-tirkar da ke tsakaninsu, don ganin cewa dalibai sun koma azuzuwansu.

An shafe watanni daliban na zaune a gida, bayan gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami’o’in da gwamnatin Najeriya.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.