Latest:
Labarai

Mun Kusa Karshen Yajin Aikin ASUU- Mista Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce nan bada jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a fadin kasar nan.

Ngige ya sanar da haka ne a ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da korafe-korafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabanin kungiyar.

Ministan ya kara da cewa suna da wani zaman da ASUU a ranar Alhamis, da zimmar kawo karshen tirka-tirkar don suga cewa dalibai sun koma azuzuwansu.

Idan ba’a manta ba, an shafe watanni daliban jami’o’i na zaune a gida saboda yajin aiki, wanda ASUU ta shiga saboda zargin gwamnatin Najeriya da gaza biya mata bukatunta kamar yadda suka yi yarjejeniya a baya.

Leave a Reply