Home Labarai Babu shiga ba fita a fadar shugaban kasar Nijar

Babu shiga ba fita a fadar shugaban kasar Nijar

 

A Jamhuriyar Nijar, dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun tsare duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a riga an tantance ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi fama da juyin mulki bayan samun ƴanci daga turawan mulkin mallaka a 1960, inda aka yi juyin mulki har sau huɗu.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito cewar masu tsaron fadar shugaban ƙasar sun toshe duk wata hanya ta zuwa gidan shugaban ƙasa da ke birnin Yamai, amma babu wani rahoto na zirga-zirgar sojoji ko harbin bindiga.

Haka nan lamurra na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

A shekara ta 2021 ne aka zaɓi Bazoum a matsayin shugaban ƙasar ta Nijar.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.