Home Labarai Bidiyon Dala: Muhuyi Ya Yi Sammacin Ganduje

Bidiyon Dala: Muhuyi Ya Yi Sammacin Ganduje

Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi sammacin tsohon gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje domin bada bayani game da bidiyon Dala.

A shekarar 2017 ne jaridar intanet ta Daily Nigerian, ta wallafa wasu jerin bidiyoyi dake nuna Gwamna Ganduje ya na cusa Dalar Amurka a aljihunsa.

A cewar jaridar kuɗin cin hanci ne amma Gwamna Ganduje ya musanta.

Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.