Labarai

Cibiyar Hulda Da Jama’a Ta Kasa Ta Taya Daya Daga Cikin Mambobinta Murna Bisa Nadin Da Gwamna Bala Mohammed Yayi Masa

Cibiyar hulda da jama’a ta NIPR reshen jihar Bauchi ta yabawa gomnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad a bisa nada mambarsu Mohammed Sani Muhammad na kwalejin kimiyya da fasaha na Abubakar Tatari Ali dake nan Bauchi a matsayin magatakarda na farko a makarantar horarwa kan harkokin man fetur ta Petroleum training institute dake Alkaleri na jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar ta NIPR reshen jihar Bauchi Alh Kabir Ali Kobi shine yayi wannan yabon a yayinda yake taya sabon Mai rikon mukamin magatakardan ,inda ya bayyana nadin amatsayin abunda ya dace la’akari da irin kwarewa da Yake dashi.

Kabir Kobi yace nadin na Mohammed Sani Mohammad Wanda shine sakataren sashin kwamitin Bada shawari na cibiyar ,yace wannan na daga cikin sakayya akan jajircewarsa da Kuma sadaukar dakai da yakeyi a bakin aiki ,inda ya bukaceshi daya daure akan haka domin ganin ya sauke wannan nauyi da gomnan jihar Bauchi ya daura masa.

Shugaban cibiyar ta NIPR ya Kuma amfani da damar wajen taya murna wa sabon Shugaban makarantar Dr Ahmed Sulaiman Yaro tareda sauran jami’an makarantar a bisa samun wannan damar.

Leave a Reply