Home Labarai Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ƴan ta’adda 39 da cika hannu da...

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ƴan ta’adda 39 da cika hannu da 159 

Dakarun sojin Najeriya sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton ɓauna, inda suka kashe 39 daga cikinsu tare da kama 159 a jihohin Borno da Yobe.

Daraktan yaɗa labarai na shalkwatar tsaron ƙasar Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin wani taron manema labarai a shalkwatar tsaron ƙasar da ke Abuja.

Manjo Janar Edward Buba, ya ce dakarun ƙasar sun sha alwashin ci gaba da fatattakar mutanen da ke yi wa zaman lafiyar ƙasar zagon ƙasa.

Daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron ya ce dakarun sojin saman ƙasar sun ƙaddamar da hare-hare ta sama kan gungun ‘yan ta’adda a dajin Sububu da ke Kankara a jihar Katsina, tare da wargaza sansanoninsu.

Ya ƙara da cewa dakarun rundunar Hadin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabashin ƙasar, sun kama manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a garuruwan Gwoza da Tarmuwa da ke jihohin Borno da Yobe.

Manjo Janar Buba ya ce farmakin da sojojin suka kai ya tilasta wa wasu ‘yan ta’addan ajiye makamansu tare da kuɓutar da wasu mutane da mayaƙan suka kama da ƙwato makamai masu yawa.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.