Home Labarai Dokar Zaɓe Ba Ta San Da Mataimakin Dan Takara Na Riƙo Ba...

Dokar Zaɓe Ba Ta San Da Mataimakin Dan Takara Na Riƙo Ba – INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta yi watsi da batutuwan da wasu ƴan takarar shugaban ƙasa suke yi cewa sun bayar da sunayen waɗanda suka zaɓa mataimaka a matsayin na riƙo.

A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a Najeriya, ɗaya daga cikin Kwamishinoni na INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa babu batun ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na riƙo a kundin tsarin mulki.

Ya bayyana cewa tuni duka ƴan takarar shugaban ƙasa suka bayar da duka sunayen mataimakansu ga hukumar INEC, ba wai mataimaka na riƙo ba.

Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa inda jama’a da dama ke ganin me zai sa wasu daga cikin ƴan takara su aikata wannan kuskure.

Ko a kwanakin baya sai da Tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso ya shaida wa kafar BBC cewa ya bayar da sunan wani mutum a matsayin mataimakinsa na riƙo ba na dindindin ba.

Ya bayyana cewa nan gaba idan ya kammala tuntuɓa da sauran masu ruwa da tsaki za su tura wa hukumar INEC sunan mataimaki na dindindin wanda zai maye gurbin wanda suka saka a yanzu.

Kazalika, a kwanakin baya an yi ta raɗe-raɗin cewa shi ma dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sunan Kabiru Ibrahim Masari, wani dan siyasa dan asalin Jihar Katsina, a matsayin mataimakinsa na riƙo.

Sai dai Tinubu ya fito ya bayyana cewa an zaɓi Kabiru Masari ne, amma zai iya sauka zuwa wa’adin da hukumar zaɓe ta bayar yana mai cewa hakan bai saɓa wa doka ba.

 


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.