Latest:
Labarai

Shugaba Buhari Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Bisa Daukar Doka A Hanu

Shugaba Muhammadu Buhai na Najeriya ya gargaɗi ƴan ƙasar da su guji gaggawar mayar da martani ko ɗaukar mataki, ko jawo fargabar da za ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi, sakamakon yaɗuwar bidiyo dabam-dabam na kisan ƴan arewa a kudu maso gabashin Najeriya, da ake zargin ƙungiyar IPOB da aikatawa.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Buharin kan yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa “a yayin da hukumomin da suka ƙware ke ƙoƙarin gano gaskiyar zarge-zargen da ke ƙunshe cikin hotuna masu ɗaga hankalin da ake yaɗawa, muna kira ga dukkan ƴan ƙasa da su guji gaggawar ɗaukar matakan da za su ƙara rikita al’amarin, sannan su bi doka ta hanyar barin hukumomi yin abin da ya dace.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma gargaɗi jama’a kan su guji yaɗa abubuwan da ba su da tabbas a kan sahihancinsu a shafukan sada zumunta, don durƙusar da masu burin son ganin an samu rarrabuwar kawuna da jawo rikici.

A ƙarshe shugaban ƙasar ya yi tur da Allah-wadai da “kisan gilla da ake yi wa mutanen da ba su ji ba su gani ba” a Kudu maso Gabashi da ma sauran sassan ƙasar.

Ya bayyana irin waɗannan kashe-kashe a matsayin “masu matuƙar ɗaga hankali”, tare da gargaɗin masu aikata hakan da cewa su tsammaci tsattsauran martani daga jami’an tsaro.

Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne dai suka kashe matar mai suna Harira Jibril, mai shekara 32, da ƴa’ƴanta Fatima, mai shekara tara, da Khadijah, mai shekara bakwai, da Hadiza, mai shekara biyar, da Zaituna, ‘yar shekara biyu da wasu aƙalla mutum shida a jihar.

Ƴan sandan Najeriya sun tabbatar da kisan inda suka ce suna neman waɗanda suka aiwatar da wannan aika-aika.

Kafar BBC ta tattauna da mijin matar mai suna Jibril Ahmed wanda a cewarsa matar tasa wadda ke ɗauke da cikin wata tara na hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai tare da yaransu Orumba North wanda a hanyar ne aka tare su aka kashe su.

Alhaji Usman Abdullahi wanda shi ne Sarkin Hausawan Ihiala a Anambra shi ma ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce matar asalin ƴar Jihar Adamawa ce daga arewacin Najeriya.

Sarkin Hausawan wanda yanzu haka yake gudun hijira ya ce al’ummar Hausawa na cikin wani hali a Jihar Anambra.

A cewarsa, a Ƙaramar Hukumar Ihiala wanda a nan yake, babu wani Bahaushe da ya rage sakamakon duk sun yi gudun hijira saboda barazanar ƴan Ƙungiyar ta IPOB.

Ko a kwanakin baya sai da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kashe wasu sojoji biyu da suke shirin yin aure a Jihar Imo.Jama’a da dama a shafukan sada zumunta musamman ƴan arewacin Najeriya sun fusata sakamakon wani bidiyo da ake ta yadawa da ke nuna yadda aka kashe wata mata da yara a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.

Leave a Reply