Latest:
Labarai

Gwamnatin Jihar Bauchi Tace Zata Sanya Kafar Wando Ɗaya Da Masu Saran Bishiyoyi Don Yin Gawayi.

 

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ayyana yaƙi da masu sana’ar gawayi, inda ya gargadi masu saran bishiyoyi domin gawayi dasu daina ko kuma su fuskanci hukunci.

Gwamnan ya yi wannan barazanar ne a lokacin kaddamar da wannan gangamin dashen itatuwa da aka gudanar a rukunin gidaje na Dungal dake kan hanyar Bauchi zuwa Jos.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kara da cewa, ayyukan mutane masu sana’ar gawayi na gurbata muhalli ba tare da la’akari da wata hanya ba, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa zata zage damtse wajen dakile hakan.

Ya kuma umurci shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomi dama sarakunan gargajiya dasu rungumi dabi’ar dashen itatuwa a dukkanin fadin jihar domin ganin an ceto muhalli.

A nasa bangaren, kwamishinan ma’aikatar gidaje da muhalli Danlami Ahmed Kawule, yace aikin na dashen itatuwa za’a gudanar dashi a dukkanin gefen titi hagu da dama mai nisan kilomita 12 daga yankin Miri zuwa gidan mai na Mobil.

Ya kara da cewa za’a kuma dasa irin wadannan bishiyoyi tun daga shatale-talen Awalah zuwa filin jirgin sama mai nisan kilomita 22.

Leave a Reply