Labarai

Sojoji Sun Kama Masu Sarrafa Haramtattun Makamai A Filato

Sojoji sun bankado wata masana’antar kera makamai ta bayan fage a yankin Vom da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

“An kuma kama wasu mutum biyu da ke hada bindigogin suke kuma safararsu ,” in ji kakakin rundunar soji ta Operation Safe, Kyaftin Oya James.

Ya bayyana cewa a yayin samamen, sojojin sun kama bindigogi 6 kirar AK-47, SMG 4 da kuma pistol a haramtacciyar masana’antar makaman

Sauran haramtattun makaman sun ha hada da bodin bindigogi kirar AK; kayan badin bindigogi, kwanson albarusai, jigidan harsasai da kuma kayan kiran bindigogi.

Kyaftin Oya James ya ce sojoji za su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kamawa da kuma tabbatar da ganin masu aikata miyagun laifuka sun fuskanci hukunci.

Jaridar Aminiya