Latest:
Labarai

Gwamnatin Sojin Nijar Ta Naɗa Ministoci 21

Shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ya nada ministoci 21, karkashin jagorancin sabon Fira Ministan kasar.

 

Shugaban mulkin sojin, Janar Abdoulrahamane Tchiani ya sanar da mambabin majalisar ministocin ne a ranar da kungiyar ECOWAS za ta fara taron da za ta cim-ma matsaya kan sabon matakin da za ta dauka kan juyin mulkin Nijar din.

Tsohon madugun ’yan tawaye ya kafa kungiyar neman mai da Bazoum kan mulkin Nijar

Fira Minista Ali Mahaman Lamine Zeine da sojojin suka nada ne zai jagoranci ministocin, wadanda daga cikinsu sojoji za su jagoranci ma’aikatu shida — tsaro, harkokin cikin gida, lafiya, sufuri, muhalli da kuma matasa da wasanni .

 

Ga jerin sunayen ministocin:

Fira minista kuma Ministan Kuɗi da Tattalin arziki — Lamine Zeine Ali Mahamane

Karamin Ministan Tsaron ƙasa — Laftanar-Janar Salifou Mody

Karamin ministan harkokin cikin gida da tsaron al’umma — Birgediya-Janar Mohamed Toumba

Ministan Matasa da Wasanni — Kanar-Manjo Abdourahamane Amadou

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a — Kanar-Manjo Garba Hakimi

Ministan sufuri — Kanar Salissou Mahaman Salissou

Ministan Muhalli da Tsafta — Kanar Maizama Abdoulaye

Ministar Ilimi da Koyar da Sana’oin Hannu da Bunƙasa Harsunan ƙasa — Elizabeth Cherif

Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan — Aissatou Abdoulaye Tondi

Ministan Jin Kai da Agajin Gaggawa — Aissa Lawan Wandarama.

Ministan Harkokin Waje da Haɗa kan ’Yan Nijar Mazauna Ketare — Bakary Yaou Sangare

Ministan Kula da Majalisar ƙasa da Tabbatar da Lafiyar Cikin Gida — Soumana Boubacar

Ministan Noma da Kiwo — Mahaman Elhadj Ousmane

Ministan Ilimi Mai Zurfi da Binciken Kimiyya da Fasaha — Farfesa Mahamadou Saidou

Ministan Shari’a da Kare ’Yancin Dan-Adam — Alio Daouda

Ministan Tsare-tsaren da Samar da Gidaje — Salissou Sahirou Adamou

Ministan Man Fetur da Ma’adinai da Makamashi — Mahaman Moustapha Barke

Ministan Yawon Buɗe Ido da Sana’oi — Guichen Agaichata Atta

Ministan Sadarwa da Bunƙasa Fasahar Zamani — Sidi Mohamed Raliou

Ministan Kasuwanci da Masana’antu — Seydou Asman

Ministan Harkokin Kuɗi a Ofishin Firaminista — Moumouni Boubacar Saidou

Hakan kuwa na zuwa ne washegarin da Janar Tchiani ya karbi bakuncin Khalifan Darikar Tijjaniyya na yakin Yammacin Afirka, Malam Muhammadu Sanusi II a birnin Yamai, bayan gwamnatin sojin ta ki amincewa da ziyarar wakilan ECOWAS da kasashen duniya domin sulhu.

A farkon makon nan ne sojojin suka nada tsohon ministan kudin kasar, Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin fira minista, kimanin mako uku bayan sun kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, da har yanzu suke tsare da shi.

Leave a Reply