Latest:
Labarai

Tinubu ya bukaci  malamai su koma Nijar a karo na uku

 

Shugaba Bola Tinubu ya umarci ayarin malaman addinin Musulunci da ke shiga tsakani a rikicin Jamhuriyar Nijar su koma wajen shugabannin mulkin sojin ƙasar don samo wani ƙwaƙƙwaran alƙawari.

Bayan wani taron sirri da malaman, jagoran tafiyar, Ustaz Abdullahi Bala-Lau ya ce Tinubu na neman a kauce wa amfani da ƙarfi don warware rikicin, kuma a tabbatar an mayar da Nijar kan tafarkin tsarin mulki.

Ya ce Tinubu ya karɓi shawarwarinsu na a kauce wa amfani da ƙarfin soja wajen kawo ƙarshen duk wata taƙaddama, musamman ma a tsakanin maƙwabta da manyan ƙawaye na tsawon lokaci.

A ranar Laraba ne, malaman addinin Musuluncin suka koma Nijar a karo na biyu, inda suka gana Shugaba Abdurahamane Tchiani da Firaminista Ali Lamine Zeine, kafin su dawo Abuja don yi wa Shugaba Tinubu bayani a kan matsayar da suka cimma.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Sheikh Bala-Lau ya ce: “Wannan ce ta sa ya sake cewa mu koma Nijar don mu ci gaba da tattaunawa a ƙoƙarin ganin an mayar da ƙasar kan tsarin dimokraɗiyya.

Ya kuma umarci mu sake tuna wa shugabannin sojin Nijar cewa akwai fa shawarar da Ecowas ta yanke game da juyin mulki”.

A cewarsa, kwalliya ta biya kuɗin sabulu a shiga tsakanin da malaman suka yi, abin da ya sa har shugabannin mulkin sojin suka karɓi masu shiga tsakani na ƙungiyar Ecowas ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar da Mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III.

Shehin malamin ya ce za su koma Nijar ne don ci gaba da tattaunawa, don kuwa sun fahimci cewa jazaman yaƙi ya kasance zaɓi na ƙarshe.

BBC Hausa

Leave a Reply