Labarai

FCTA Ta Rusa Kasuwar Dare Da Ke Asokoro, Abuja 

 

Jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja FCTA, a ranar Talata sun rusa wata haramtacciyar kasuwa mai suna “Kasuwan Dare”, wacce ta kasance maboyar masu laifi da masu sayar da muggan kwayoyi a Asokoro, Abuja.

Kasuwar ta kasance akan titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Asokoro Extension.

Daraktan Sashen Kula da Cigaban birnin, Mista Mukhtar Galadima, ya bayyana cewa haramtacciyar kasuwar ta zama barazana ga mazauna yankin da masu wucewa.

Ya kara da cewa, bata-gari da ke gudanar da ayyukansu a yankin suna yin illa ga kyawon muhallin baki daya, inda ya kara da cewa, Hukumar ba za ta lamunta ba a ci gaba da hakan.

Jaridar Leadership

Leave a Reply