Gwamnatin Tarayya ta ce daga yanzu ba za sake sanya cibiyoyin kwararru ba a cikin kasafin kudi ba da zai suma daga ranar 1 ga watan Junairun 2024.
Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Ben Akabueze ne ya bayyana hakan a wata wasika da aka rabawa manema labarai.
Sanarwar Wanda aka fitar ranar 26 ga Yuni, shekara ta 2023 ta bukaci wadanda abin ya shafa da su fara yin gyare-gyare da wuri domin su ci gaba da tafiyar da kungiyoyinsu ba tare da wata matsala ba bayan da gwamnati ta janye tallafin kudi.
A halin da ake ciki, daga yanzu za a ɗauke su a matsayin cibiyoyi masu cin gashin kansu don su kasance da cikakken alhakin ma’aikatansu, da kuɗin da ake kashewa, da kuma kashe kuɗi.
Akabueze ya ce matakin ya yi daidai da shawarar kwamitin shugaban kasa kan albashi (PCS).
Sai dai da yawa na kallon matakin a matsayin wani sabon yunkuri na gwamnatin tarayya na rage kashe kudade.
Akwai cibiyoyi sama da 30 na kwararru a Najeriya, inda wasu daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke ba su tallafin sun hada da hukumar rijistar malamai ta kasa (TRCN) da hukumar shirya zarabawa ta (NECO) da kuma hukumar shirya jarrabawar Afrika ta yamma (WAEC) a karkashin ma’aikatar ilimi,da kuma, cibiyar watsa labarai ta kasa wato Nigerian Press Council da dai sauransu.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.