Labarai

Ta Haihu A Hanun Masu Garkuwa Da Ita

Daya daga cikin fasinjojin da ‘yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.

Tashar talabijin ta AriseTV wadda ta wallafa wannan labarin ta kuma ce wani dan uwan matar ne ya sanar da su haka.

Dan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake rike da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.

“Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gomman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da ‘yan ta’addan suka gayyaci likitoci su karbi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba,” inji dan uwan matar.

A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.

Leave a Reply