Labarai

Gwamnoni zasu iya yafiya ko biyan tara wa farsunoni cewar Gwamnatin tarayya a ƙoƙarinta na rage cinkoso a gidajen gyaran hali

 

Gwamnatin tarayya ta ce gwamnoni zasu iya yafiya ko kuma biyan tarar da ke kan fursunoni wanda baiyi kasa da naira miliyan daya ba.

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da Asibiti mai gadaje 20 a babban gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Patakwal.

Aregbesola yace a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke nemo maslaha ta dindindin ga matsalar cinkoso a gidajen gyaran hali da tarbiyya, gwamnatocin jihohi zasu iya tallafawa ta hanyar biyan kananan basussuka da tarar da ke kan fursunoni a gidajen gyaran hali da tarbiyya tare da gina karin kotuna a cikin gidajen gyaran hali da tarbiyya don harzarta yanke hukunci.

Yace wasu daga cikin mazauna gidan gyaran hali da tarbiyyar sun samu kansu a wannan hali ne saka kananan laifuka da jihohi zasu iya yafewa.

Ministan ya kara da cewa ba da jimawa ba ha umarci kontirolan hukumar kula da gidajen gyaran hali da tarbiyya kan ya hada jadawalin sunayen fursunoni da suk shigo gidan sakamakon bashin da bai wuce naira miliyan daya ba, wanda gwamnatocin jihohi ya kamata su biya musu.

Ya ce kimanin mutane dubu biyar ne aka samu a cikin wannan jadawali, kuma sun jima matuka a gidan gyaran hali da tarbiyya karkashin kulawar gwamnati, kuma ana kashe musu kudin abinci sama da abin da ake binsu a matsayin kudin tarar da zasu biya jihohi.

Leave a Reply