Labarai

Manchester City ta lashe FA Cup

Manchester City ta dauki Kofin FA bayan ta doke Mancheter United da ci 2-1 a wasan da suka yi ranar Asabar.

Ilkay Gundogan ne ya zura dukkan kwallayen biyu, lamarin da ya sa Manchester City ta lashe kofi na biyu a kakar wasan bana ya zuwa yanzu.

Tuni dai City ta dauki Kofin Gasar Firimiya, don haka yanzu abin da ya rage mata shi ne Kofin Zakarun Turai inda za ta fafata da Inter Milan a makon gobe a Istanbul don nemansa.

Idan ta lashe shi za ta bi sahun United, wadda a 1999 ta lashe kofuna uku.

TRT Afrika

Leave a Reply