‘Yan kasuwa a Ghana sun yi barazanar rufe shagunan su a ranar Litinin mai zuwa saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar na cedi.
‘Yan kasuwar sun ce darajar kudin kasar ta fadi sosai idan aka kwatanta da dala abin da ke ja musu kashe kudade sosai wajen shigo da kaya.
Sun ce a kowacce rana idan suka je siyan kaya ko kuma wajen biyan kudin fito to sai sun tarar komai ya tashi.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar kasar, Joseph Obeng, ya ce karin harajin da ake yi wa ‘yan kasuwa shi ke janyo tashin farashin kayayyaki.
Shugaban ‘yan kasuwar ya ce ba wai za su rufe shaguna don su musguna wa jama’ar kasar ba ne, sai dai don su ja hankalin gwamnati a kan halin da ake ciki a kasar.
Rahotanni sun ce tsadar rayuwa da kuma hahhawar farashin kayayyaki a Ghana ya kai fiye da kaso 31 cikin 100, adadi mafi girma a cikin shekara 20 a kasar.
Gwamnatin kasar dai a koyaushe na dora alhakin halin da kasar ke ciki a kan annobar korona da kuma yakin Rasha da Ukraine.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.