Home Siyasa Idan Naci Zabe Zan Gyara Harkar Tashohin Jirgin Ruwa –Kwankwaso

Idan Naci Zabe Zan Gyara Harkar Tashohin Jirgin Ruwa –Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce ba zai bari a lalata harkokin tashoshin ruwa yadda aka saba ba idan aka zabe shi a 2023.

Ya ce Najeriya na bukatar ingantaccen tsari a ɓangaren teku domin ta kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Mista Kwankwaso ya kuma yi kira da a gaggauta gyara tare da rage cunkoso a hanyar shiga tashar ruwa ta Apapa a jihar Legas.

Ɗan takarar shugaban ƙasa r na jam’iyyar NNPP ya yi wannan kiran ne a wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar ruwa da kamfanin Prime Maritime Project ya shirya a Legas a yau Talata.

A cewar Kwankwaso, lallai kasar nan na bukatar ta tsara yadda za a samu ci gaba a fannin teku domin yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.