Jama’atu Nasiril Islam (JNI) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da kuma hukumomin sojin kasar da su yi adalci, su hukunta wadanda suka kashe Sheikh Muhammad Goni Aisami cikin hanzari.
Cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ta JNI Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu, kungiyar ta jaddada cewa tilas a dauki matakin ladabtarwa kan masu hannu a wannan kisan.
Sai dai ya kara da cewa hukumomin Najeriya su daina kawar da kai kan wadannan jerin kashe-kashen da a yanzu suka zama ruwan dare, “Muna da karfin gwuiwa cewa ana kitsa wadannan kashe-kashen ne da gangar.”
JNI ta kuma ce “duk da cewa sojoji biyun da aka kama, wato John Gabriel da Adamu Gideon, sun hada baki domin sace motar malamin addinin Islaman, al’ummar Musulmi ba su fito sun tuhumi ‘yan ta’adda Kirista da kai wa Musulmi hari ba, wanda da Kirista aka kai wa irin wannan harin, da tuni kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta fara kururuwa cewa Musulmi sun halaka wani fasto ko rabaran, sannan da tuni kafofin yada labarai sun cika shafukansu da labarin.”
Sanarwar ta kuma ce kisan da aka yi wa Sheikh Aisami alama ce ta yadda aikata manyan laifuka ya kai ga dukkan sassa na kasar nan, har ma ya kai ga jami’an tsaro, wadanda aikinsu ne su kare rayukan al’umma.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.