Jakadan Faransa a Nijar zai ci gaba da zama a cikin kasar duk da matsin lamba daga sojojin da suka yi juyin mulki, in ji Shugaba Emmanuel Macron.
Macron a jawabinsa ga jakadun kasashen waje ya jaddada goyon bayansa ga hamɓararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum wanda ya ce ba zai yi murabus ba.
A cewar Macron wannan matakin ya nuna Bazoum mutum ne mai karfin hali.
Wa’adin sa’o’i 48 da aka bai wa jakadan Faransar, Sylvian Itte domin ya bar Nijar ya riga ya cika.
Macron ya kara da cewa Faransa ba za ta canza matsayinta ba na yin Allawadai da juyin mulkin soji a Nijar tare da nuna goyon bayanta ga Bazoum.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.