Daga Fa’izu Muhammad Magaji
Wata Kutun shariâar Muslunci mai lamba biyu da ke zama a birnin Bauchi ta Éaure wani tashi tsawon shekaru biyu a gidan Yari, bayan samun sa da laifin sace wasu kayyakin amfanin wani masallaci a jihar Bauchi da ke Gabashin Najeriya.
Matashin mai suna Lawan Mohammad, Éan kimanin shekara 25 a duniya wanda yake zama a anguwar Kur da ke Bauchi an gurfanar da shi gaban kotun ne bayan Ƴan Sanda sun kama shi da zargin sace kayyakin masallacin.
Kayan da aka yi zargin ya sata sun haÉar da Jannareto, da Æimar kuÉin sa ta kai Naira dubu Éari biyu da kuma man fetur lita goma wanda kuÉin sa ya kai Naira 6200.
Matashin ya kuma saci Fanka ta sama, wadda kuÉin ya kai Naira 15000, kuma Æ´ar yawo wato Estetion wanda ta kai Naira 5000, sai kuma kofar daya Éalle wadda kuÉin gyaranta ya kai Naira 20,000.
Mai karanta Æara ya faÉawa kotun cewa bayan ya sace kayyakin ne, ya tafi wata unguwa da Karuwai ke taruwa wadda ake kira Bayan Gari ya kama Éaki tare da karuwansa, ya tayar da Jannareton masallacin suka cigaba da shaÆatawa, da Fetir Éin masallacin.
Bayan an karantawa matashin laifin da ake zargin sa da shi gaban kotun, nan take ya amsa laifin sa, inda Alkalin kotun Barrister Mukhtar Adamu Bello Yamban, ya yanke masa hukumci Éaurin shekara biyu ba tare da zabin biyan tara ba.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








