Home Labarai Zamu haÉ—a kai da gwamnoni don tantance bayanan talakawan Najeriya – Edu

Zamu haÉ—a kai da gwamnoni don tantance bayanan talakawan Najeriya – Edu

Ministar harkokin jin-Æ™ai da kawar da talauci ta Najeriya, Betta Edu ta ce gwamnatin Æ™asar za ta yi aiki kafaÉ—a-da-kafaÉ—a da gwamnonin jihohi, da Æ™ananan hukumomi da kuma shugabannin al’umma domin tantance cikakkun bayanan talakawan Æ™asar.

Misis Edu ta bayyana haka ne ranar Juma’a a lokacin hira da gidan talbijin na Channels.

Ta Æ™ara da cewa gwamnati za ta yi hakan ne domin cimma burin ma’aikatar jin-Æ™ai ta Æ™asar na fitar da miliyoyin ‘yan Æ™asar daga Æ™angin talauci.

”Abu na farko da za mu fara yi, shi ne tantance rajistar sunayen masu Æ™aramin Æ™arfi ta Æ™asar, domin tabbatar da cewa talakawan ne a cikinta, waÉ—anda suka cancanci shiga cikin rajistar,” in ji Ministar jin -Æ™ayin.

Ta ci gaba da cewa a ‘yan makonnin baya-bayan nan an yi ta samun ce-ce-ku-ce daga É“angaren Æ™ungiyar gamnonin Æ™asar da sauran Æ™ungiyoyi, kan ingancin rajistar.

“Wasu na cewa ta yi, wasu kuma na cewa ba ta ba, saboda mutanen da ke cikinta, ba su ne suka cancanci shiga cikinta ba, an shigar da siyasa cikin wajen haÉ—a rajistar”, in ji ta.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.