Labarai

An sace sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar APC reshen Kaduna 

 

Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne yi awon gaba sace Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna, Kawu Ibrahim Yakasai.

An sace Kawu Yakasai wanda shi ne tsohon Shugaban Karamar Hukumar Soba ne a gidansa da ke kauyen Yakasai.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 zuwa10 a daren Juma’a bayan maharan sun yi ta harbe-harbe a cewar majiyoyinmu da ke a yankin.

Hakan na faruwa ne kasa da mako guda bayan masu garkuwa da mutane sun sace Kansilan Gundumar Garu a Karamar Hukumar ta Soba, Alhaji Sabitu Ahmad a gidansa.

Daya daga cikin shugabannin jam’iyar APC a Jihar ta Kaduna wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da nuna damuwarsa a kan matsalar tsaro a yankin.

Ya kuma yi fatan Allah Ya kubutar da shi da sauran mutane da ke a hannun masu garkuwa da mutane cikin aminci.

Sakataren Yada Labaran gwamnan jihar, Muhammad Lawal Shehu ya tabbatar da lamarin, inda ya ce gwamna Uba Sani ya umarci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin ceto Alhaji Yakasai cikin aminci.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply