Labarai

Kotu ta daure wani mutum tsawon shekara ɗaya bisa kwashe shinfiɗu da agogon wani Masallaci a Kano

 

Kotun shariar musulunci dake zamanta a ɗanbare karkashin jagorancin Mai Shari’a Munzali Idris Gwadabe ta yankewa wani mutum hukuncin ɗaurin shekara ɗaya Babu zaɓin tara, bayan samunsa da laifin kwashe shinfiɗun masallaci da kuma agogon bango na wani masallaci dake unguwar Ɗorayi a jihar Kano.

Tunda fari dai ‘Yan sanda ne suka gurfanar da Kabiru Abdullahi ‘yan ƙusa bisa kunshin tuhumar shiga waje ba tare da iziniba da sata.

Mai gabatar da ƙara Bashir Wada Aliyu ya karanto masa tuhumar, kuma ya amsa laifinsa hakan yasa aka yanke masa hukuncin.

Freedom Radio

Leave a Reply