Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 5 a ranar Litinin ta tabbatar da kwace Masallacin Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam tare da garkame shi.
Kacewar ya biyo bayan daukar dogon lokaci ana tafka shari’a inda daga bisani ta kwace Masallacin da ke unguwar Sabuwar Gandu.
An kwace Masallacin ne kacokan daga hannun kungiyar Izala, kotu ta mika shi ga kungiyar ci gaban unguwar ta Sabuwar Gandu.
Kamar yadda lamarin ya kasance, da safiyar ranar Litinin, Alkalin babbar kotun mai lamba 5 da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako, Mai Shari’a Malam Usman Na’Abba ya je Masallacin na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, da ke unguwar ta Sabuwar Gandu da kansa, domin jaddada hukuncin da kotun ta yi watanni uku da suka gabata na tabbatar da mallakin Masallacin da makaranta da kuma gidan liman ga kungiyar ci gaban unguwar ta Sabuwar Gandu da kewaye.
A wata takarda mai dauke hatimin kotun har ma da na mai shari’a mai dauke kwanan watan 18 ga Mayun wannan shekara da muke ciki, Alkalin kotun ya shaida cewa, duba da shekaru da aka shafe ana gudanar da shari’ar tsakanin unguwar ci gaban unguwar da kuma kungiyar Izala, a don hakan ne ma shaidu daga kowane bangare sun tabbatar da cewa fili da kuma gine-ginen mallakin kungiyar ci gaban unguwar ta Sabuwar Gandu ne, wanda kuma a wancan lokaci kungiyar Izala ta gaza gamsar da kotu da hujjoji masu kwari dangane da da’awar da take yi na mallakin wannan Masallaci har dai da makarantar, don haka ne ma alkali Malam Umar Na’abba ya yi umarnin cewa daga waccan rana ta biyu ga Fabrairun wannan shekara da muke ciki, kotu ta tabbatar wa qungiyar unguwar ta Sabuwar Gandu mallakinsa sabanin kungiyar Izala da take da’awa tun a baya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa an like kofofin masallacin da takardun umar kotu da take umarnin cewa babbar kotun ta mika mallaki da kuma iko na wannan masallaci ga qungiyar ci gaba unguwar. An gano motar Izala a harabar Masallacin na kwashe kayan masallacin da kuma shirye-shirye kwashe kayan gidan limamin domin bin umarni kotu.
An shafe shekara bakwai ana shari’ar tsakanin kungiyar Izala, da gwamnatin Kano da kuma babban sakataren ma’aikatar kasa da tsare-tsare da kungiyar ta ci gaban unguwar, amma yanzu komai ya zo karshe.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.