Latest:
Labarai

Hajjin Bana: Filin Jirgin Saman Gombe Zai Yi Jigilar Alhazai

Jami’an Hukumar Kula Da Filayen Jiragen Sama Ta Kasa (NCAA), sun ziyarci Jihar Gombe, inda suka duba Filin Jirgin saman kasa da kasa na Gombe da kayan aikin da ke ciki, a ci gaba da shirye-shiryen fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar zuwa kasa mai tsarki ta Saudi Arabiyya.

Kwamitin mai mambobi hudu karkashin jagorancin Kwanturolan sufurin jiragen sama, Ango Shehu kuma manajan shiyya na hukumar a ofishinta na Kaduna, ya bayyana gamsuwa da nagartar kayan aikin da ke filin jirgin, inda ya yaba wa gwamnatin Jihar Gombe karkashin jagorancin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa yadda ta kara inganta filin jirgin.

Ya ce bisa nazari da binciken da suka yi, filin jirgin saman na kasa da kasa na Gombe, ya kimtsa tsaf don fara jigilar aikin Hajjin bana.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, wadda ya tarbi kwamitin a madadin, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gode wa hukumar ta NCCA bisa ziyarar dubiyar, yana mai bada tabbacin cewa gwamnatinsa na ci gaba da kula da filin jirgin don kyautata ayyukansa.

Leave a Reply