Home Labarai Layin Dogo: Majalisar Zartaswa Ta Kasa Ta Amince Da Sama Da Naira...

Layin Dogo: Majalisar Zartaswa Ta Kasa Ta Amince Da Sama Da Naira Miliyan 700 Wa Tsaron Layin Dogo A Abuja

Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da Naira miliyan 718.19 don tabbatar da tsaron layin dogo na birnin tarayya Abuja mai tsawon kilomita 45 da wasu tashoshi 12.

Ministan babban birnin tarayya Abuja Mohammed Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar a ranar Laraba.

Matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na baya-bayan nan ya biyo bayan harin da aka kai kan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna wanda ya kai ga dakatar da ayyukan sufurin jirgin.

A harin da aka kai a watan Maris, ‘yan bindigar sun dasa bama-bamai tare da kai wa fasinjoji hari, wanda yayi sanadin mutuwar wasu tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Watanni bayan faruwar lamarin, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta iya ci gaba da aikin jirgin kasan ba.

Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ya ce irin wannan matakin ba zai rasa nasaba da halin da iyalai da ‘yan uwansu ke tsare ba.

A cewarsa, gwamnati na binciken irin kayan aikin tsaro da ya dace a sanya don saka ido sosai kan hanyoyin da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da ba da rangwame wa tsarin haɗin gwiwar na PPP.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.