Harkokin kula da lafiya sun sake gamuwa da cikas a asibitocin gwamnati a Najeriya, sakamakon yajin aikin da ma’aikatan lafiya suka shiga na sai-abin-da-hali-ya-yi.
Ma’aikatan wadanda ba su kunshi likitoci da jami’an jinya ba wato nas-nas, a karkashin hadaddiyar kungiyar JOHESU, sun dauki wannan mataki ne a fadin kasar saboda batutuwan da suka shafe albashi da kuma kula da jin dadinsu.
Gamayyar kungiyar ta ce ta bai wa gwamnati wa’adin mako biyu domin biya wa ma’aikatan bukatunsu amma kuma ba abin da aka yi.
Ma’aikatan su ne ke kula da bayanan marassa lafiya da dakunan gwaje-gwaje da sauran ayyuka a asibitocin gwamnati a Najeriya.
Yajin aikin ya tilasta wa wasu marassa lafiya tafiya asibitocin ƴan kasuwa, marassa hali kuwa sun rasa na yi, wanda hakan ke jefa rayuwar wasu da dama cikin hadari.
Kari a cikin bukatun ma’aikatan suna son ba tare da bata wani lokaci ba, gwamnati ta amince a rika biyansu da tsarin albashin ma’aikatan lafiya na gaba-daya da biyansu bashin kudaden alawus-alawus da suke ba shi ma nan da nan tare kuma da sake tsarin shekarun yin ritaya daga aiki.
JOHESUN ta shiga wannan yajin aiki ne kwana hudu bayan da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aikinta na gargadi na kwana biyar domin bai wa gwamnati mako biyu ta aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.