Home Labarai Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Janye Yajin Aiki

Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Janye Yajin Aiki

Ma’aikatan wutar lantarki na Najeriya sun janye yajin aikin da suka tsunduma ranar Laraba wanda ya kai ga jefa ilahirin kasar cikin duhu.

Kungiyoyin ma’aikatan lantarkin dai da suka hada da NUEE da SSAEC sun amince su janye yajin aikin ne bayan wani zaman tattaunawa da suka yi da Ministan Kwadago, Chris Ngige a ranar Laraba.

Ministan dai ya kira ma’aikatan ne zaman tattaunawa na gaggawa tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya don a magance batutuwan da suka kai ga shiga yajin aikin.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.