Home Labarai Majalisar Dattawa ta ƙaryata zargin tsige Akpabio

Majalisar Dattawa ta ƙaryata zargin tsige Akpabio

 

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi watsi da maganganun da ke yawo kan cewa wasu ‘yan majalisar na son tsige shugabanta Sanata Godswill Akpabio.

A wata sanarwa da majalisar ta wallafa a shafinta na X (Twitter a baya), majalisar ta ce duka labaran karya ne.

A cikin ‘yan kwanakin nan wasu jaridun Nijeriya suka ruwaito cewa wasu sanatocin kasar suna shirya makarkashiya ta yadda za su tsige Sanata Akpabio.

Jaridun sun ce Sanatocin har sun yi wata tattaunawa ta musamman a Saudiyya da kuma Jihar Kwara duk a yunkurin tsige shugaban majalisar.

Sanarwar da mai magana da yawun Majalisar Dattawan Nijeriya Yemi Adaramodu ya saka wa hannu ta bayyana cewa:

“An jawo hankalinmu kan wasu rubutun shaidanci a wasu kafafen watsa labarai, kan wani zargi mai kama da mafarki na sauya shugabancin Majalisar Dattawa.

“Majalisar Dattawan Nijeriya tsintsiya ce madaurinki daya. Wannan kirkirar na daga cikin labarin karya kan biyan kowane dan majalisa naira miliyan 100. Yana da kyau a san cewa Majalisar Dattawa ta goma, karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio tana gudanar da ayyukanta na dokoki da kundin tsarin mulki yadda ya kamata,” in ji sanarwar.

Kawo hargitsi

Majalisar Dattawan Nijeriyar ta ce akwai wasu wadanda ba a cikin majalisa suke ba da ke son kawo rudani ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta inda ta gargade su kan hakan.

Haka kuma ta bukaci a bar ta domin ta sarara ta yi ayyukan da suke gabanta ta yadda za a matsar da Nijeriya gaba.

Majalisar ta kuma gargadi kafafen watsa labarai kan cewa kada su bari a rinka amfani da su wurin watsa labaran karya.

A cikin wannan watan na Satumba ake sa ran majalisar za ta koma bakin aiki bayan dogon hutun da ta tafi na makonni.

TRT Afrika Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.