Home Labarai Majalisar wakilai ta nemi a kara albashin malaman Firamare zuwa N250,000, Sakandire...

Majalisar wakilai ta nemi a kara albashin malaman Firamare zuwa N250,000, Sakandire N500,000, lakcarori N1m

 

Habubakar Fulata, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i ya yi kira da a kara albashi ga malaman Firamare, Sakandare da Jami’o’i.

Shugaban ya ce ya kamata ya tu malamain firamare su rika daukar Naira 250,000, Sakandire N500,000 da kuma Naira miliyan 1 ga malaman jami’o’i a duk wata.

Mista Fulata yana magana ne a wajen wani taron bita na kwana daya na masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa taswirorin tsarin ilimi na Najeriya (2023-2027), a Abuja a yau Alhamis.

Fulata ya ce yana da kyau malaman Najeriya su kara kwarin gwiwa ta hanyar biyan su kudaden da suka dace domin koyar da yara.

Ya kuma jaddada wajibcin fassara dukkan litattafan darussa zuwa harsunan cikin gida domin kamo matakin tsarin na duniya.

A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun yi kokari a fannin ilimin kasar amma hakan bai haifar da sakamakon da ake so ba.

Daily Nigerian Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.