Latest:
Labarai

Anyi wa wata mata yankan rago a Gombe 

 

Wasu da ake zargin ’Yan Kalare ne sun yi wa wata mata mai ’ya’ya takwas yankan rago a garin Gombe.

Maharan sun shiga gidan Malama Aishatu Abdullahi mai shekaru 58 ne a daren Juma’a, suka yi mata yankan rago a unguwar Jekadafari

Wani rahoto da Aminiya ta samu daga hadimin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kan sha’anin tsaro da harkokin gwamnati, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, ya ce ana kyautata tsamnanin turo su aka yi su kashe matar.

Ya bayyana cewa maharan sun shiga gidan Malama Aishatu ne da misalin karfe 9 na dare aka yi mata yankan rago sannan suka tsere da wayar salularta.

Hadimin gwamnan ya ce bayan faruwar lamarin an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka ziyarci gidan suka dauke ta zuwa asibitin kwararru na jihar.

Kakakin ’an sandna jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a lokacin da ’yan sandan suka isa gidan marigayiywar sun tarar da ita kwance male-male cikin jini, suka dauke ta zuwa asibitin inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Jami’in ya ce, kwamishinan ’Yan Sanda Mai Kula da Ayyukan, Hayatu Usman a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ba da umarnin a gagguata fara bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Ya kara da cewa rundunar ba za ta zauna ta nade hannu miyagun abubuwa irin haka na faruwa ba, don haka sai sun zakulo wadanda suka aikata laifin dan fuskantar shari’a.

Daga nan sai yace dokar nan da aka sanya ta takaita zirga- zirgar jama’a daga karfe 12 na dare ta na nan ba canji.

Jaridar Aminiya