Ministar jin kai, Hajiya Sadiya Umar Faruk ta ce akalla mutane miliyan 1.7 ne ke fama da bakin talauci da rashin muhalli, sakamakon ibtila’i daban-daban a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ministar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, a jawabinta ga taron da ta yi da jagororin ma’aikatar, kan shirin karfafa tafiya da kowa wajen inganta tsarin rayuwar ’yan Najeriya.
“Duk da samun tashe-tashen hankulan dole ne ya jefa mutane da dama cikin tsananin talauci, muna duba hanyoyin inganta aikin wannan ma’aikatar tamu.
“Yanzu haka alkaluma mutane miliyan 1.8 ne suka rasa muhallansu, sakamkaon aukuwar bala’o’i, da tashe-tsashen hankula, hadi da ayyukan ’yan ta’adda.
“Hakazalika akwai irinsu matsalar dumamar yanayi da mabaliyar ruwa, wadanda su ma sun taimaka wajen jefa ’yan Najeriya da dama a mawuyacin hali.
“Shriye-shiryenmu a yanzu karkashin tsarin NSIPs sun hada da N-Power da na ciyar da dalibai da na ba da jari ga kamfanoni, manoma da daidaikun mutane
“Sauran sun hada da na tsarin ‘Cash Transfer’, wadanda muke fatan za su rage wannan matsalar.
“Tun bayan kafa ma’aikatar a shekarar 2019, ba ta taba sauka daga kan dalilin kafa ta ba,” in ji ministar
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.