Home Labarai Mutum 79 ne suka riga mu gidan gaskiya bisa hatsarin mota cikin...

Mutum 79 ne suka riga mu gidan gaskiya bisa hatsarin mota cikin wata 10 a Gombe – FRSC

 

 

Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Gombe, ta ce mutum 79 ne suka mutu a hatsarin mota 278 da suka faru daga farkon watan Janairu zuwa 31 ga Oktoban 2023.

Kwamandan hukumar a Jihar, Felix Theman ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Gombe, lokacin da yake kaddamar da wani gangami na musamman kan bukukuwan karshen shekara.

Theman ya ce taken gangamin na wannan shekarar shi ne, “Gudun wuce sa’a yana kisa, a yi tuki cikin nitsuwa kuma a guji daukar kaya fiye da kima.”

A cewar shi, mutum 779 sun ji munanan raunuka a lokacin hatsarin, kodayake alkaluma sun nuna cewa yawan hatsarin yanzu ya ragu sosai.

“A shekarar 2022, hukumar ta tattara bayanan hadura, 445 mutum 110 suka mutu, inda 1,074 suka ji raunuka,” in ji Kwamandan.

Ya kuma ce jami’ansa sun kama mutum 4,665 bisa karya dokokin hanya 5,098 cikin watannin 10 a faɗin jihar.

Daga nan ya ce laifuffukan da aka kama mutanen da su sun hada da daukar kaya fiye da kima da kin sanya na’urar rage gudu da rashin sanya lamba da tuki ba tare da mallakar lasisi ba da makamantansu.

Da yake jawabi yayin gangamin, Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, cewa ya yi gwamnati ta damu da lafiyar direbobi kuma tana matukar bukatar ganin suna amfani da hanyoyi yadda ya kamata.

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Manasseh Daniel Jatau, ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ta himmati wajen gina hanyoyi da sanya fitilun kan titi masu aiki da hasken rana a kwaryar garin Gombe da kewaye domin jama’a.

Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.