Home Labarai Shugaba Buhari zai karrama zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa da mataimakinsa da lambar girma...

Shugaba Buhari zai karrama zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa da mataimakinsa da lambar girma GCFR da GCON

 

A ranar Alhamis 25 ga watan Mayu na shekarar 2023 ne ake saka ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karrama zababben shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Za a basu lambar girman babban kwamandan askarawan Najeriya wato GCFR, da kuma na GCON wa Kashim Shettima.

Hakan na kunshe ne cikin wata takaitacciyar sanarwa da mai tallafawa shugaban kasar na musamman kan kafafen sadarwar zamani Tolu Ogunleai ya wallafa ta kafar sadarwa na Tuwita.

Acewar Ogunlesi, a ranar, za a mika takardun mika mulki wa gwamnati mai zuwa.

A nasa ra’ayin wannan shi ne zai zamo mika mulki mafi tsari da zaman lafiya a tarihin Najeriya, wanda dokar Executive Order ta goma sha hudu da shugaban Buhari ya sanyawa hannu ta tanadar.

Da yake tabbatar da bada lambar girma na GCFR wa shugaban kasa mai jiran gadoda ta GCON wa mataimakin shugaban, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa za a gudanar da wannan biki a dakin taro da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Babban sakataren gwamnatin, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin mika mulkin ya ce a ranar Alhamis ne za a gabatar da makala mai taken karfafa demokradiyya don samar da ci gaba,wanda tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai gabatar a ranar Asabar 27 ga watan Mayu.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.