Home Siyasa Shugaban Jam’iyyar APC Ya Gargadi Bashir Machina

Shugaban Jam’iyyar APC Ya Gargadi Bashir Machina

Shugaban jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu, ya gargadi Bashir Machina, da ke cewa shi ne dan takarar sanata mai wakiltar Yobe ta arewa a APC, a kan ya shiga taitayinsa.

Abdullahi Adamu, ya yi wannan gargadin ne a yayin da yake kare matakin da jam`iyyarsu ta dauka na mika sunan shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ga hukumar zabe a matsayin dantakarar sanata mai wakiltar Yobe ta arewa maimakon Bashir Machina.

Shugaban jam’iyyar ta APC, ya gargadi Machina da cewa ya yi hattara domin maganganun da yake fadi sun fara neman su yi yawa.

Ya ce,” Ni a matsayina na shugaba na san babu wata doka da jam’iyya ta karya, domin babu wata doka da ta ce idan ka shiga wata takara ba za ka shiga wata ba, don haka ba dokar da ta hana shi ko ta hana kowa ma.”

Sanata Abdullahi Adamu, yayi wannan maganar ne bayan da mutumin da ke takarar sanata karkashin inuwar jam’iyyar APC a Yobe ta Arewar, wato yankin da shugaban Majalisar Dattawan kasar ke wakilta ya ce har yanzu shi ne ɗan takarar mazabar na APC.

Dan takarar sanatan Bashir Machina, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da take ƙasa take dabo game da makomar siyasar shugaban Majalisar Dattijan Najeriyar, Ahmed Lawan, bayan ya rasa takarar shugaban ƙasa a APC da ya nema.

Sanata Ahmed Lawan       Bashir Machina

Tun bayan kammala zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC dambarwa ta kunno kai kan yiwuwar rasa takararsa ta sanata bayan ya shafe fiye da shekara ashirin yana wakiltar al’ummarsa a Majalisun Tarayyar ƙasar.

Rahotanni a baya-bayan nan sun yi ta yaɗa cewa Sanata Ahmad Lawan ya samu takarar ɗan majalisar da yake kai yanzu, sai dai mutumin da ya ci takarar tun da farko, Bashir Sharif Machina ya ce har yanzu shi ne ɗan takarar Sanatan Yobe ta arewa a jam’iyyar APC.

Kuma an yi ta samun bayanai da rade-radi da ake ta yadawa cewa wasu jiga-jigan APC na neman tursasa wa ɗan takarar ya janye wa Ahmed Lawan.

A lokacin Bashir Machina, ya ce ya fitar da takarda a shafukan intanet wanda ya aike wa jam’iyya, kan tuntubar da aka yi masa ko yana nan kan takararsa.

Ya ce shi kuma ya amsa da cewa bai janye ba, kuma yana kan takararsa.

Sannan ya ce shi baki da baki Ahmed Lawan bai tuntube shi ba, don haka yana nan kan bakarsa kamar yadda jama’a suka zaɓe shi

Tun bayan kammala zabukan fitar da gwani da masu neman takarar mukaman siyasa sukayi, mutanen da suka faɗi zaɓen irinsu gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Kaura, ya koma neman takarsa ta gwamna a karo na biyu bayan gaza cimma muradinsa na neman takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP.

Haka a Sokoto ma an ga yadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya koma ya nemi tikitin sanata bayan rasa damar cimma burinsa na neman kujerar shugaban kasa.

Shi ma Tambuwal din ya samu ɗan takarar da, a farko aka ce shi ya yi nasara, ya janye masa.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.