Home Labarai Sojoji sun kubutar da daliban Jami’ar Gusau wadanda aka sace jiya

Sojoji sun kubutar da daliban Jami’ar Gusau wadanda aka sace jiya

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ta ceto dalibai hudu na Jami’ar Gusau wadanda aka sace a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba da dare.

Rundunar ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook inda ta ce dakarunta na Operation Hadarin Daji da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan kasar ne suka yi aikin ceton.

Sojojin sun bayyana cewa an sace daliban ne a gidan da suke zaune wanda ke wajen jami’ar a Sabon Gida da ke yankin Damba a Gusau.

Sojojin sun bayyana cewa jim kadan bayan sace daliban suka samu kiran gaggawa wanda hakan ya sa suka toshe hanyoyin da barayin za su iya sulalewa.

A cewarsu, bayan an yi musayar wuta da barayin sai suka saki wadanda suka yi garkuwa da su suka gudu.

Satar daliban na zuwa ne makonni bayan an sace wasu gomman daliban na jami’ar wadanda har yanzu babu labarinsu.

Sai dai bayan an sace rukunin farko na daliban Jami’ar ta Gusau sojojin sun ce sun yi kokarin ceto shida daga cikinsu.

TRT Afrika Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.