Home Labarai Sojojin sunyi kutse ofishin EFCC domin kwato Æ´an uwansu

Sojojin sunyi kutse ofishin EFCC domin kwato Æ´an uwansu

 

Hukumar da ke yaÆ™i da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon Æ™asa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami’an sojin saman Æ™asar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin Æ™wato ‘yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin ‘karya dokar aikin tsaro’.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai É—auke da sa hannun jami’ain hulÉ—a da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami’an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuÉ—i ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida – da suka haÉ—ar da sojoji huÉ—u da É—aliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu – waÉ—anda ke wurin a lokaci da aka kama waÉ—anda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna Æ™awanya da nufin tilasta sakin mutanen.

”Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.

Dele Oyewale ya ce a ranar Juma’a wasu jami’an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faÉ—a, don tilasta sakin abokan aikin nasu.

“Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga Æ™arshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an É—auki bayansu”, kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.