Labarai

Wadanda aka musu rigakafin Covid-19 ne kawai zasu gudanar da aikin hajjin bana – Gwamnatin Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta bayyana cewar wadanda aka musu cikkekken allurar rigakafin cutar covid-19 ne Kawai zasu gudanar da aikin hajjin wannan shekarar .

Babban sakataren hukumar jindadin alhazai na jihar Bauchi, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris shiya sanar da hakan lokacin da yake amsa tambayoyi kan kiwon lafiyar mahajjata.

Yace a aikin hajjin bana, dole ne dukkanin maniyata su karbi allurar rikafin cutar kamar yadda gwamnatin kasar Saudiyya ta bayar da umurni.

Jami’in Hulda da jama’a na hukumar, Muhd Sani Yunusa, ya bayyana cewar, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris ya shawarci maniyata dasuyi kokarin yin allurar domin kaucewa fadawa matsala.

Dayake tsokaci kan mata masu juna biyu, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris ya shawarcesu dasu dage zuwa aikin hajjin a wannan shekarar domin kaucewa jefa rayuwarsu a garari.

Ya kuma nanata cewar hukumar jindadin alhazai na jihar Bauchi ta kammala dukkanin shirye shirye domin tantance maniyyatan, yana mai Kara da cewar mata masu juna biyu bazasu aikin hajjin ba, kamar yadda doka tayi bayani.

Leave a Reply