Bankin Duniya ya ce akwai kyakkyawan fatan cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar 2023.
Bankin ya kuma ce Najeriya za ta iya alkinta kudin da yawansu ya kai Naira tiriliyan 3 da biliyan 900 a shekarar ta bana kadai, sakamakon garambawul din da Gwamnatin Tarayya ta yi wa tsarin tattalin arzikinta.
Sabbin matakan gwamnatin dai tun bayan rantsar da Bola Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya sun shafi canjin kudaden kasashen ketare da kuma dakatar da ci gaba da bayar da tallafin man fetur.
Babban jami’in da ke wakiltar bankin a Najeriya, Alex Sienaert, ne ya yi wannan hasashe yayin gabatar da wata mukala kan lamurran tattalin arziki a Abuja.
Hasashen bankin ya ce yana sa ran karuwar karfin tattalin arzikin Najeriya da kaso 3.3 cikin 100 a bana, yayin da sai kuma a badi (2024) ake sa ran tattalin arzikin kasar ya karu da kaso 3.7.
Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban Kasa ne dai Tinubu ya sanar da soke biyan kudaden tallafin man fetur, shirin da kididdiga ta nuna cewar a shekarar bara kadai sai da ya lakume wa gwamnati Dala biliyan 10.
Makonni kadan bayan cire tallafin man ne kuma, gwamnatin ta Tinubu ta mayar da tsarin canjin kudaden kasashen ketare zuwa na bai daya, abin da ya sanya darajar Dalar Amurka daya ta haura Naira 700.
Sai dai a yayin da Bankin Duniyar ya yaba da matakan da Najeriya ta dauka, ya yi gargadin cewar al’ummmar kasar za su fama da hauhawar farashin kayayyaki, kalubalen da ya ce na takaitaccen lokaci ne, domin al’amura za su daidaita zuwa nan gaba. (RFI)
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.