Wata mahaifiya ta sami nasarar kama wanda ya yi garkuwa da ’yarta a wajan kai kudin fansa.
Sai dai bayan ta kama shi an gano cewa tuni ma har ya kashe ’yar tata kuma ya birne gawarta a gidansa da ke Karamar Hukumar Zariya a jihar Kaduna.
Binciken Aminiya ya gano wanda ake zargin mai suna Aminu Ibrahim mai shekaru 35 da haihuwa, ya yi garkuwa da Fatima Adamu mai shekara 23 da haihuwa, kuma ya kashe ta inda ya birne gawar a gidansa.
Wakilinmu ya ziyarci gidan da lamarin ya faru a layin Sadauki da ke gundumar Wusasa a Zariya, inda ya tattauna da mahaifiyar mamaciyar mai suna Nana Fatima.
Nana, wacce ta yi bayani cikin kuka ta ce, “Sati hudu da ’yata Fatima ta yi tafiya zuwa Kaduna suna, iuma tace ba za ta wuce kwana hudu ba.
“To bayan tafiyarta sai muka dinga kiran wayarta ba ta shiga, sai daga baya wani ya dauka ya ce wai Fatima tana wajensu kuma sai an ba shi Naira miliyan 3 kafin su sake ta.
“Daga nan ne muka gane cewa Fatima dai an yi garkuwa da ita ne.”
Nana Fatima ta kara da cewa to bayan sun fahimci haka sai suka kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke Dan Magaji a Zariya.
Ta ce, “Bayan haka muka fara ciniki da wadanda suka kama ta har dai suka ce a kawo musu abin da ke hannunmu, inda na nemo Naira dubu dari da ke hannuna sannan muka yi mahada na kai musu kudin,” in ji Nana.
Sakamakon neman karin kudi da suka yi, Nana Fatima ta ce sai ta sa wani filinta a kasuwa domin sayarwa don ta haɗa kudin amma sai ba a sami mai saye ba har dai daga baya ta iya sake hada Naira dubu dari.
Ta ce daga nan sai ta kira mai garkuwa da mutanen inda ta sanar da shi cewa ta sake hada wasu kudin, kuma ya umurce ta da ta kai masa.
Ta ce, “To a wannan karon sai muka tafi da kanwa ta Hajara domin mu kai kudin, to muna tafiya muna waya da shi har ya ce mu zo kofar asibitin Wusasa, da ke Zariya can kuma sai ya ce mu dawo baya haka muka yi ta yi har muka hadu da shi tun da dama ni na san shi.
“Bayan haduwar mu sai yayi kokarin ya kwance kudin a hannuna amma na ki yarda tun da cikin mutane ne, to dama ya riga ya sauka daga kan babur din da ya kawo shi.
“Ana cikin haka sai na kwada ihu jama’a barawo don Allah a taimake ni. Nan da nan kuwa jama’a suka yi ca aka kama shi.
“Daga nanne aka kai shi ofishin ’yan sanda, inda ya yi bayanin yadda ya kashe ’ya ta Fatima sannan suka birne ta suka dora buhunan gawayi a inda suka rufe ta,” inji ta.
Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da kama wanda ake zargin, sannan ya ce ya kuma kai jami’an ’yan sanda inda ta birne gawar.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.