Wasu ’yan bindiga sun harbe manoma biyu har lahira sannan suka jikkata wasu da dama a gonarsu da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.
Kauyukan da aka kai wa hare-haren sun hada da Shuwaka, Unguwan Bagudu da kuma Sabon Layi.
Bayanai sun nuna an kai harin ne wajen misalin karfe 11:30 na safe, lokacin da galibin mazauna kauyukan ke aiki a gonakinsu.
Wadanda aka kashe din su ne Alhaji Yahaya Shuwaka da kuma Fadaman Gaude.
Mazauna yankin sun ce an kai musu harin ne saboda mutanen sun ki biyan harajin da ’yan bindigar suka dora musu, har wa’adin ya cika.
A cewar Ishag Kasai, Shugaban Kungiyar Ci Gaban Masarautar Birnin Gwari (BEPU), ya tabbatar da kai harin, inda ya ce an kai musu harin ne bayan cikar lokacin ba su biya kudin ba.
Ya ce, “Idan za a iya tunawa, ’yan bindigar sun sanya wa manoman yankin harajin Naira miliyan 10, kuma wa’adin biya zai cika ne ranar 30 ga watan Mayun 2023.6.5”
“Tun bayan cikar wa’adin maharan suka fara farmakar manoman yankin a gonakinsu da gidajensu.
“Har yanzu muna rokon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kawo mana dauki. Matsalar ita ce kamar yadda muka fuskanta a baya, ko da an biya harajin, ba za su daina kai mana hare-haren ba.”
Sai dai jaridar Aminiya ta ganon cewar saboda fargabar da suke da ita, yanzu haka manoman na fargabar zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a kashe su, alamarin da ake fargabar zai iya haifar da karancin abinci a yankin.
Wadanda aka ji wa raunukan dai a yanzu haka suna can suna samun kulawa a wani asibiti da ke yankin. Wannan dai shi ne karo na biyu da maharan ke kai farmaki yankin a cikin makon nan.
Duk kiraye-kirayen da wakilinmu ya yi wa Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna don jin ta bakinsa a kan lamarin ya ci tura saboda bai amsa kiran wayarsa ba.
Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.