Wasu ’yan kungiyar asiri sun fille kan wani Babban DPO Mai Kula da yankin Ahoada da da ke Karamar Hukumar Ahoada ta Jihar Ribas.
’Yan kungiyar asirin sun fille kan DPO mai suna CSP Bako Amgbasim ne a lokacin da ya jagoranci ’yan sanda suka kai samame maboyar ’yan wata kungiyar asisi mai suna Icelanders.
Mazauna yankin sun bayyana cewa cewa ’yan kungi’yar asirin sun yi musayar wuta da DPOn da jami’ansa.
Maja’yarmu ta ce ana cikin haka ne harsasan ’yan sandan suka kare, shi ne ’yan kungi’yar suka yi musu kwanton bauna suka cafke su, suka kakkashe.
A wani bidiyo da wakilin Jaridar Aminiya ya gani, an nuna gangar jikin marigayin, inda aka ji muryar wasu na caccakar sa bisa karfin halin DPO Bako Ambasim na yin fada da ’yan kungiyar asiri ta Icelanders.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ta tababar da faruwar lamarin.
Karamar Hukumar Ahoada ta Jihar Ribas ta yi kaurin suna wajen ayyukan kungiyoyin masu gaba da juna.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.